RAYUWAR ASMAU CHAPTER 7
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 7 Haka rayuwa ta cigaba dan gashi har Asma’u sun fara exam. Murna suke dan baza su dawo skul ba asibiti zasu tafi su zama student doctor. Sun gama Exam lafiya. Inda suka koma gida suna shan hutun su. Dady kuwa har ya dawo an gama hada mata asibitin ta. Bangaren Yaa Aslam kuwa sai wata kulawa da ya dada bata. Dan shakuwar su ta koma yawa yanzu haka ma zai zo wani aiki zai yi sati daya a kano. Murna gun Asma’u kamar me? ************ Bangaren Sabir kuwa, duk ya damu bama da akai hutun nan baya samun damar ganin Asma’u. Mamah ta rasa me yake damun sa dan ba karamin sauyawa yayi. Duk yadda Mamah taso ya fada mata damuwar sa ki yayi sai dai ya ce ba komai. Zaune yake akan kujera dake garden din gidan su. Idonsa a lunshe sai sake saken yadda zai ga Asma’u yake. Can ya mike zaune da sauri yana lalubar number wayar Maryam. Kira yayi sai da ta daga suka gaisa sannan ya ce, “Daughter number wayar *Husnah* nake son ki bani.” “Ohk bari na turo maka.” Ta katse wayar tana murna dan tin da taga …