RAYUWAR ASMAU CHAPTER 4
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 4 Washe gari kamar yadda ta tashi tin asuba ta tashi.+ Sallah tayi ta zauna tai karatun al kur’ani sannan ta janyo littafin ta ta kara dubawa ta jima tana duba littafin sannan ta mike ta sauka kasa. Mami ta dan kamawa abubuwa ssannan ta koma sama. Wanka tayi ta shirya cikin wata maroon kalar doguwar riga mai dogon hannu. Golding din takalmi da jaka ta dauka sai bakin hijab da ta saka iya kar sa kirji. Ba karamin kyau tayi ba fuskar ta tayi fes a ciki. Idonun ta sun kara gaske da girma girar nan tata a kwance luf luf. Leben ta sai kyallin man lebe yake. Dakin Dady ta shiga suka karya sannan tai musu sallama ta fito ta tafi dakin Ya Buhari. Yana zaune a gaban system ta same shi. Karasawa tayi ta ce, “To su Yaya me ake aka tashi da sasafen nan.”” Bai kula ta ba. Dan durkusawa tayi ta gaishe shi. amsawa yayi yana dagowa ya kalle ta. Baki ya tabe ya ce “Baki kyau ba.” Murmushi tayi ta ce, “Kyan kaga nayi.” “Ahakan?” Kai ta gyada masa. “Uhmm dauki abonki afirij.” Ya fada yana nuno mata…