RAYUWAR ASMAU CHAPTER 3
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 3 ._ ________________________ Asma’u sai sha biyu da rabi ta dawo. a gajiye ta dawo ga rana. Tana shigowa gida Mami ta tare tana “oyoyo ‘yar ta” Murmushi tayi ta karasa gun Mamin ta, ta zauna a gefen ta. ta ce, “Mami sannu da gida!” “Yauwah Asma’u ya makarantar?” Asma’u ta ce, “Lafiya Alhamdulillah!” Mikewa tayi ta ce, “Mami bari naje na watsa ruwa.” “Toh!” Tayi sama, tana shiga ta ajiye jakar ta, ta cire kayan ta ta sakale su ta shiga bandaki. Ta jima tana watsa ruwa sai da taji sanyi sannan ta cuda jikin ta. Tana fitowa ta saka wata doguwar riga mara hannu. Hijab ta saka ta tada sallah. Sai da ta idar sannan ta shafa mai ta shafa hoda. Wayar ta dake ta kara tin tana bandaki ta dauka. Yaa Aslam ne dan haka da sauri ta dauki wayar ta kara akunnen ta. Sai da yai sallama ta amsa sannan ya tambaye ta ya makaranta. Dan yanzu ya kira Mami ta ce yanzu ta dawo. Da wayar a kunnen ta, ta sauka kasa dan samar abu me sanyi. Ice cream ta dauko a firij din dake kitchen din su, sannan ta dawo falo…