RAYUWAR ASMAU CHAPTER 2

RAYUWAR ASMAU CHAPTER 2
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 2 Da wuri ta kamala abinda zasuyi ta shirya tayi wajen Dadyn ta. Tare sukai break, sannan ta tafi. Da wuri ta shige ajin su. Text din Ya Aslam ne ya shigo. “Morning Pretty nah. Ya kike tin dazu nake son kiran ki. Nasan kina aiki. in kingama ki turon hoton ki. Sannan naje Lagos ne Dady ya aike ni. Ina bukatar addu’ar ki.” Murmushi tayi ta maida masa da sakon. “Na tashi lafiya Yaya nah. Kaima ina fatan kana lafiya. Ya hanya. Hotona yana can na tura maka yana jiran ka.” Ta tura tana murmushi, Zee ce ta taba ta, “Sis Lafiya kike ta zuba murmushi haka.” “Lafiya lou wallahi. Kin karaso kenan.” “Eh!” Dai dai shigowar malamin su. Sai karfe sha biyu ya fita wani ya shigo yai musu awa daya sannan suka tafi sallah. Suna fito wa suka shiga cafeteria suka siyo lemo da snack, a nan kofar hall din su suka zo suka zauna. Karkashin wata bishiya. A jaka suka saka abincin su dan ba lokacin zasu ci ba, kawayen su ne suka karaso wajen su uku. “Ah *Asmy* da Xee.” Su ka fada suna dariya. Murmushi suk…