RANA DAYA CHAPTER C KARSHE
RANA DAYA CHAPTER C KARSHE Nazeefah de bata da aikin da yafi kiran Safiyya kullum tana tambayarta mey Amal ta girka wa Afzal, shin idan ya dawo daga aiki mey sukeyi, suna yawan fita ne ko kuwa zama suke a gida suna wasa? Komai so take tana ji haka kawai tayita tada wa kanta hankali. Kwana bibbiyu Afzal ya cigaba da yima kowaccensu, bada dad’ewa ba aka bud’e makaranta. Ranan da kwanan Amal ne kuma tana da early morning lectures tare suke shiri su fita se yayi dropping nata kafin ya wuce office haka ma idan kwanan Nazeefah.+ Yau Amal da Afzal suka cika wata d’aya da aure se kuma Allah yayi ranan ya fad’o a kwananta se rawa jikinsa yake he can’t wait to go back home. Itama Amal bata mance da wannan muhimmiyar rana ba, morning lectures nata na k’arewa wajajen sha d’aya driver’n da Afzal ya mata hiring ya dawo gida ta shiga kitchen yayinda Safiyya ke tayata aiki. Abinci kala-kala suka had’a da juices abin se wanda ya gani ga fruit salad ba abinda babu dam suka cika kan dining table d’in da k…