RANA DAYA CHAPTER B

RANA DAYA CHAPTER B
RANA DAYA CHAPTER B Rawa bakinta yake tana kakkarwa tace, “Ummi wallahi ban yi mishi komai ba wallahi bani bace.”+   “Da Allah rufa mana baki!” Mummy ta katse ta. “A jinki bama sane ne da kalan rashin hankalin da kikeyi masa a gidan? Tun yaushe yaron nan yake hak’uri dake? Gashi nan k’arshenta kin sanya masa ciwon zuciya amma karki damu komi yazo k’arshe Allah tada kafad’an shi ya rubata miki takardan sakinki ki huta shima ya huta kowa ma ya huta.”   “Mummy dan Allah kar kiyi mun haka wallahi inason Afzal kuma wallahi ni ba ni bace sanadin wannan rashin lafiyan nasa Ummi you’ve got to believe me” ta juyo tana kallon Ummi a raunane “Ku tambayi D’anladi me gadi wallahi ahaka muka tsince sa a d’akinsa dan Allah ku yarda dani” sede ba wanda yako kalleta a cikinsu ita kanta Ummi kuka takeyi. Mummy ko ta had’a tagumi tana tunanin yadda zata fara sanar da Daddy wannan labari me d’aci.   “Dr dan Allah kuyi duk abinda ya kamata ku tabbata d’ana ya rayu shi kad’ai gareni bazan iya rasa saba dan Al…