RANA DAYA CHAPTER A
RANA DAYA CHAPTER A “Ban ce kibar min sharri ba?” Ya tambaya yana nad’e hannuwanshi akan faffad’an k’irjinshi.+ Cike da shagwa6a tana murza idonta tace, “Ka fad’a amman wallahi ba sharri bane wayyo Mami na ni ka kaini gun Mami na.” “Kin rantse de baza ki kulle wannan k’aton bakin naki daya cika ma mutane kunne da ihun banza da rashin kunya ba ko? Nasan yadda zanyi hakan” gano bakin zaren wato so yake ya sake ta6ata yasa tayi tsit. “Ki miqe nace” ya buk’ace ta. “Wai ba kada kunne ne? Ce maka akayi zan iya miqewan? Inda zan iya ai da nayi da jimawa ko jinka nid’in jin dad’in zama gu d’aya da kai ne? Dubi fa k’afa ka karya min.” “Kika sake cewa na karya miki k’afa sena go6e wannan fitsararren bakin naki try me and see” ya fad’a threateningly. “Azzalumi” ta furta can k’asa-k’asa yadda baze ji taba sede shegen nisan kunne ne dashi tsab ya jiyota. “Kema ‘yar gudun hijira kawai” ya mayar mata. Harara ta watsa mishi tana cigaba da zum6uro bakinta, kallo ya k’are mata sannan daga bisani ya j…