NANNY CHAPTER C KARSHE

NANNY CHAPTER C KARSHE
NANNY CHAPTER C KARSHE Riƙe ƙugu Tahir yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya, gefe Ɗaya kuma Zuciyarsa na Gudu Sosai Saboda Damuwa, Ashe ce Dake gefe Ta ƙarasa Kusa da Goggo Abu Ta Zauna Kusa da Ita Kafin Tace “Goggo…”+ Ta faɗa Tana kallonta Innaro Dake Tsaye Ta Ɗora Hannu Bisa Haɓa Tana Faɗin “Wai Hakimi meke Damunshi ne..?Tunda nake Dashi ban taɓa ganin yayi irin Wannan Fushin ba..” Tahir ya waigo ya Fara Taku Zuwa Kusa da Goggo Yana Faɗin “Ranshi yana ɓace…Dole a saurara mai Har ya Sauko Da kanshi..” Ya faɗa yana Zama gefen Ashe, Dayan Hannun ya kama yana Faɗin “Goggo Don Allah Kiyi Haƙuri kibar kukan nan Haka nan Nayi miki alƙawarin Komai zai Daidaita Insha Allahu…” Ya faɗa yana Kallonta Goggo Ta Murmusa Tana kallon Tahir da Ashe kafin tace “Bakomai…Allah yayi muku albarka Ku Tashi ku Tafi kubi Umarnin Mahaifinku..” Ta faɗa Tana ƙoƙarin Ɓoye Hawayen Da Suka Taru acikin ƙwayan Idanuwanta. Innaro ta saki Numfashi Tana Faɗin “Shine kawai magana Don Rashin Tafiyar Naku ma Matsala ne, ku Tashi ku…