NANNY CHAPTER A

NANNY CHAPTER A
NANNY CHAPTER A *KADUNA*+ _Area:Anguwan Rimi Gra_    Misalin karfe 9:30pm Daidai na Daran Ranar Asabar,ya baro Office dinsa,Direbansa Garzali ne ke Jansa Cikin Bakar Motarsa Bugatti. Hon ya Zuba akofar Tamkamemen Get din gidan nashi Mai kama da Aljannar Duniya,Megadinsa Habu ya Rugo da Gudu yazo ya Wangalemusu get Domin yasan Yallabai ne ya Dawo Adaidai Wannan Lokacin. Lokacin da Motar Ta Sulala parking Space kafin Tagama Daidaita Zama Sai ga Wasu kyakyawan Yara Guda Biyu mace Da Namiji Wadanda Ashekaru bazasu Haura Shekara goma ba Tsawonsu Daya Kuma kamaninsu Daya,sai dai mace Tafi Jiki da Kuma Tsukakkiyar Fuska yayinda Namiji yake Siriri Ammh Fuskarsa nada Fadi,Farare Tas kamar Ka Taba Jini ya Fito akallon Farko zaka musu ka Fahimci yaran yan gayu ne na Karshe Kodaga ganin yanayin Kayan Kantin Dake Jikinsu Riga da Wando da Kuma yanayin Fatarasu na Jin Dadi ne. Da gudu suka isa jikin Motar Suka Bude Bangaren Baya Suna Fadin”Wlcm Daddy…”Atare na Kallesu na sake sai alokacin Naga Dimple din…