ZUCIYA CHAPTER 25 KARSHE

ZUCIYA CHAPTER 25 KARSHE
ZUCIYA CHAPTER 25 KARSHE Bayan Ashraf ya farfado ‘yan sanda suka zagayeshi aka fara mai tambayoyi, hankalinsa akwance yake amsawa nan ya sanar dasu akan sako kanwarsa tamai ya kuma nuna musu sakon. Nan suka bukaci anuna musu kanwar. Ya sanar dasu tana gida. Kb ya jasu suka nufi gidan. ******** A bangaren Kawu kam tunda wadanda yasa aiki suka sanar dashi cewa ‘yan sanda sunzo hankalinsa yai kololuwa gun tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro da fargaba duk sun dameshi. ‘yan sanda sun shigo nan suka tsaya daga waje suka umarci a kira musu Little. Ba’a dade ba sai gatannan, tsoro duk ya kamata, me zaisa ‘yan sanda su nemeta. Bayan ta iso ogan cikinsu ya kalleta fuskarnan a hade rike da littafi yace “Ke kika turama Yayanki sako akan kina san ganinsa?”+ Cikin mamaki tace ” a’a.” Yace ” ina wayarki?” Hankalinta a kwance ta mikamai, ya duba wayar babu sakon, ya kalleta yace ” ki tuna sosai ina kika ajiye wayarki? Ko kuma wa kika ba?” Tace ” ni ban ajiyeta a ko ina ba,…