ZUCIYA CHAPTER 24

ZUCIYA CHAPTER 24
ZUCIYA CHAPTER 24 Mikewa yai daga zaman da yake tare da furzar da wata iska sannan ya d’au wayarsa yama Nafi da mumy sako akan su shirya saboda tafiyarsu. Nafi kam kallan sakon take tayi, duk da tana masifar san zuwa kasa mai tsarki sai dai abin ya zo mata a ba zata, na farko ga bikin Jibiya wanda ya matso daf sannan ita a iya saninta Hajj ake fara yi tunda shine farilla. Sai dai taci alwashin yima Ashraf magana in ya dawo. ********* Sai Yamma ya fito daga office station ya wuce inda acan ya samu Umma, kana ganinta kasan tana cikin wani halin kusa da ita ya karasa yace ” Umma lafiya?” Hawaye ne ke zubowa a idanta tace ” Ashraf banga alama Mansir nada niyyar taimakama Asim ba, na sanshi sarai akan dukiyarsa zai iya hakura da Asim a matsayin d’ansa ni kuma na tattare dukiyata naba Asim ya sa a kudin company din da ya siya.”+ Ashraf yai shiru tabbas ganin halin da take ciki ya sa ya tausaya mata sai dai bazai taba yin bailing Asim ba dan kuwa shine key dinsa na kama Ubansa. …