SOYAYYAR MU CHAPTER 3
SOYAYYAR MU CHAPTER 3 “No one can compete with you on being you. Most of life is a search for who and what needs you the most” ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇ Ta isa gida a jiqe yayin da ta danganta jiqewar da rashin samun abun hawa kuma ta nemi Zaid da Salma a waya domin a zo a dauke ta amma babu network ga kuma dare nayi wanda yasa kawai tayi tahowarta. Bayan sun koma daki ne ita da Salma ne ta bata labarin ainihin abinda ya faru tun daga farko har qarshe. Salma dai ta fara tsorata da al’amarin domin har ce ma Aisha tayi ta bar aikin saboda kada Aliyu ya salwantar mata da rayuwa, amma kuma ita Aishan ta qi, cewa ma tayi yanzu ta fara aikin. Babu yadda Salma bata yi da ita ba amma ta qi dole ta haqura ta qyale ta.+ ************ Aliyu cikin motar shi a kan hanyar komawa gida wuraren qarfe takwas bayan an gama meeting din wanda yayi shi a jiqe, yana tuqi yana tuno abinda ya faru. A zahiri Aliyu mutum ne mai bala’in tausayi, dalilin mugun tausayi irin nashi ne ko kuka baya so ya ga mutum yana y…