SOYAYYAR MU CHAPTER 1
SOYAYYAR MU CHAPTER 1 “Don’t be pushed around by the fears in your mind. Be led by the dreams in your heart” ◇◇◇◇◇◇◇◇◇ KATSINA STATE Ta iso qofar gidansu dake layin shagari avenue a cikin garin Katsina inda take ƙoƙarin sauke jakar ta ‘yar madaidaiciya ta tafiya (trolley) daga ‘yar ƙurƙurar da tayi shata tun daga tashar mota ta garin katsina inda ta sauka. Bayan ta biya shi kuɗin shi yayi gaba ne ta ja jakar ta nufi cikin gidansu. Tafe take cikin sauri domin cike take da kewar ‘yan gidan nasu. Sanye take cikin baqar jallabiya ta zamani qirar Dubai wadda ‘yan mata suke yayi.+ Takalmin da ke qafar ta mai tudu ne irin wanda ake kira wedge baqi sannan ta nada gyalen jallabiyar a kanta. Tana sanye da madubin ido a fuskar ta don kare rana. Maigadin su Malam Rabi’u shine ya dauko mata jakar ta har qofar falon su, ta karba tare da yi mishi godiya. Ko da tayi sallama ta shiga gidan babu kowa a falon don haka ne ta nufi dakin da ya kasance nasu ita da yayar ta. Shigan ta dakin ke da…