MRS AMIDUD CHAPTER 2
MRS AMIDUD CHAPTER 2 “Fito kinji babu abinda zai miki.” “Humm kawai ki kore hi zan fito.” Dafe goshinta Hajiya Adawiyah tayi sannan tace. “Yi hakuri fito,na Kore shi.” Dakyar tafito daga bayan kujera, tana zare idanunta. Zauna da ita tayi akan kujera, aikuwa ta buga tsalle sai da Yaran gidan suka fashe da dariya. “Buhayyah kalli abin dariya.” Wacce aka kira da buhayyah, murmushi tayi sannan ta mika mata hannu, tace. “Parih! Har kin manta damu ne! Aarib! Wannan arusa kin tunashi kika ce haka kuke kiran katu a Dabji, sai Ni kika ce idan da a Dabji nake me kyau za a kirani, sai Amrozia. Kin tunamu” Rau-rau tayi da idanu sannan cikin kankanuwar Murya tace. “Zaki mai dani gurin Kakata wallahi daga zuwana naga Bala’in da suka fi karfina,” Dariya suka yi sannan ce. “Toh ai kin dawo kenan bazaki kuma zuwa dabji ba.” Kura musu ido tayi kafin tayi wani irin yatsuna fuska, sannan ta ware murya ta fasa musu kuka, tanayi tana …