ZUCIYA CHAPTER7
ZUCIYA CHAPTER 7 Shiru Ashraf yai a mota bayan sun fito daga Asibiti, tunani yake mai zurfi ina zai sa Nafi a makaranta? A kalaa dai shekarunsu d’aya da Little banbancinsu dai Little nada d’an jiki sai dai Nafi siririyace sosai sai tsayi, ko alphabet bata iya ba. Ya d’an juya kai, ina zai sata? Yarinyar nan dai bamai ansarta ko Js1 ne to a hakan ma Js1 ya mata kankanta saboda ita ba yarinya bace, yai d’an karamin tsaki lalai Malam dama wahala ya d’auramai. Sam baiji sanda Driver yake ta cemai Oga ina zamu? Can bayan ya gama tunani ya kalli Adamu yace “Adamu me muke jira kuma? ” Adamu ya dan saki fuska yace ” tun d’azu nake tambayar inda zamu banji kace komai ba. ” Tsaki ya kara ja sannan yace “Mu tafi gida, tunani ne suka min yawa. ” A gida kam kan kace me kowa yasan abinda Ashraf yama Aneesa akan wasiyyar da za’a bata, duk ta yad’ashi tana fadama mutane tana kukan sakalci, anyi carko carko a waje kowa nata fada’an albarkacin bakinsa, sai dai kaf Ashraf suke bama laifi gani …