ZUCIYA CHAPTER 9

ZUCIYA CHAPTER 9
ZUCIYA CHAPTER 9 Yau saura bikin Ashraf da Aneesa wata d’aya da kwana 10, a wannan ranar ce kuma Nafi ta shirya tsaf cikin uniform d’inta, Little tayi kokari wajen koya mata komai, Nafi ta fito fes da ita abin sha’awa ga kayan sunsha guga. A wannan lokacin inba fad’ama akai ba ko hausarta kaji ba tabbas bazaka gane daga riga ta fito ba, Little ta jawo a kwatinta tana cewa ” Zaki tafi ki barni ni kad’ai. “+ Nafi tai murmushi a ranta tace da ina riga bana fita, yanzu nazo nan kuma shima gashi zan koma wani gun. Little ta dafata tace ” Muje Ya Habib na jiranmu. ” Nafi ta kalleta sannan ta d’anyi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace ” Maryam bazanje inma yaya sallama ba? ” Little ta d’anyi dariya sannan tace ” kije mana, amma bada ni zaki ba, ni zanje gun Mumy inkin gama sai kizo can mu had’u. ” Nafi ta d’aga mata kai alamar eh sannan ta fito da saurinta, tana tafe tana tunanin me zata cemai, sam bata kula da Asim a zaune akan kujera ba, har ta wuceshi taji ance ” ke dan…