ZUCIYA CHAPTER 8
ZUCIYA CHAPTER 8 Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari. + Nan ya taho da shi gidansu Ashraf. Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamman ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta. Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take, sunayi suna ‘yar hirarsu da Goggo. Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d’an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace ” Wai kizo inji yaya. ” Nafi ta kalleta cikin zak’uwa tace ” Ya Ashraf? ” kai Amra ta d’aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b’angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu, tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai. Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba, sai dai yau gani tai anzo an bud’e da fara’arta ta kalli mai bud’ewa tace ” Yaya ina kwa…… “kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi. Jin ta tsaya da …