ZUCIYA CHAPTER 6

ZUCIYA CHAPTER 6
ZUCIYA CHAPTER 6 Kwanaki sun d’an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d’agawa, tana zuwa gyaramai d’aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin. + Kamar yanda ta saba yau ma a ka’ida zataje ta gyara b’angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d’au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa’in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud’e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d’aki ta d’auka ya fita, me zata gani? Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfa…