ZUCIYA CHAPTER 5

ZUCIYA CHAPTER 5
ZUCIYA CHAPTER 5 Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad’ai tace ” Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? “+ Cikin rashin kulawa da abin tace ” name fa? ” Little ta zauna a gaban madubi tace ” kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? ” Nafi ta kalleta tace ” lalai Maryam meye abin jin haushi? Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d’auka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? ” Little tai d’an karamin tsaki tace “Wlh ba wani kayansu, sannan dan ita zai aura sai akace tazo ta d’au abinda ba nata ba? ” Nafi ta mike tace ” kafin ki shirya bari na anso miki abinci. ” Bata jira amsarta ba tai waje da sauri, Little ta bita da kallo a fili tace ” lalai wato dan indaina maganar shine zaki gudu? ” Nafi kam tana fita tai murmushi tace ” ni da naga kaya daga sama? Dan an d’au d’aya menene? ” Kitchen ta wuce, ta amso abincinsu kenan zata shiga bangarensu taji ance “Ke!” Juyawa tai dan tasan Umma…