ZUCIYA CHAPTER 3
ZUCIYA CHAPTER 3 Kallansa take cikin tsananin mamaki ya sake murmushi yace ” Riga tafa? Ko kin barmin wannan d’in? ” Kasa tai da kanta sannan a hankali tace “na d’auka ka tafi ai. ” Datti yace ” me kuke nufi kenan ka santa dama? Sani bana taimako ba? ” Ashraf yad’an yi murmushi dama so yake ya kular da Datti yace ” sani kuwa tunda ji jiya a d’akin ta na kwana. ” Yai maganar yana kallan Nafi, gaba d’aya kowa ya kalleshi, Datti ya rike haba yace ” Kwana? ” Ashraf yai wani murmushin rainin hankali sannan ya ya d’aga kai yace ” Uhm hum” Hannee da mamanta suka kalli Nafi cikin mamaki, Dan litti shima mamaki ne taf a ransa lalai wannan gayen ashe dan duniya ne? Nafi ce tayi baya da sauri tai cikin gida, kallan kofar data shiga sukai suna tunanin me kuma zatai. Nafi kam tana shiga da sauri tai d’aki tana tafe tana murmushi takasa gane dalilin murmushin nata, rigarsa data ninke d’azu ta dauka abin haushi ba tada turare hakan yasa ta fito, suna tsaye sai gata ta dawo. Datti yai tsa…