ZUCIYA CHAPTER 21

ZUCIYA CHAPTER 21
ZUCIYA CHAPTER 21 Nafi ganin tana ta kiran number Ashraf amma shiru yasa ta mike tai hanyar waje da sauri, Little ta bita da kallan mamak, me ke damun Feenah? + Kitchen ta nufa da kanta ta shiga shiryama Ashraf abincin safe tana gamawa ta juye sannan ta fito tai bangarensu, wanka tai ta zura wata doguwar rigar abaya ash color anyi kwalliya da stones kalar silver a jiki, tayi kyau sosai. Little kam mamaki take tace ” ina zaki wai?” Nafi tace ” dan Allah so nake in zaki fita skul yanzu mu tafi tare ki ajiyeni a gun aikin yaya.” Idanu Little ta zaro tace ” kije kiyi me?” Tace ” gun mijina zanje, hankali na bazai taba dawowa daidai ba sai naga halin da yake ciki.” Little ta rike baki cikin mamaki tace ” lalai Feenah kinyi nisa bakyajin kira, amma kina gani yayan bazai fada ba in kika je?ki kirashi a waya tukunna.” Nafi tai ajiyar zuciya tace ” da na sameshi a waya ai hankali na bazai tashi haka ba, sannan in ma yamin fadan zuwan ai dai a kalla na ganshi, bazanji haushi ba.”…