ZUCIYA CHAPTER 20
ZUCIYA CHAPTER 20 Ashraf yana fita ya wuce gidan su Ferry, yayi sa’a kuwa a lokacin Mahaifin su Ferry ya dawo.+ Tare suka shiga gidan bayan sun gaisa Isma’il ya kalli Ashraf yace ” banyi tsammanin ganinka da wuri haka ba.” Ashraf ya dago cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace ” Kasan komai ko kuwa kaima bincike kakeyi??” Isma’il yai murmushi yace ” Bansan komai ba sai dan abinda ba’a rasa ba.” Ashraf yai dan huci kadan yace ” Auwal Max a ina zan sameshi??” Kai ya girgiza yace ” bansan inda yake ba, tun wannan ranar, in fact banmasan ko yana raye ba ko ya mutu, sai dai nasan abu d’aya tabbas shine wanda yaja Alhaji a wannan ranar sai dai abin zargi shine sun fita daga gida tare amma daga baya danai bincike sai naji Alhaji ne kawai a cikin motar sannan a bincike nane na gano Auwal Max mai gadi yana kallansa sanda ya shiga kasan mota, hasashe na ne yasa nasan yayi wani abu bawai proof gareni ba.” Ashraf ya matse hannunsa da karfi, tare da runtse ido yace ” Shi Abban a i…