ZUCIYA CHAPTER 19
ZUCIYA CHAPTER 19 Nan Dady yai ta jansa da hira shima yana biyemai kafin daga bisani yamai sallama, Habib yace “muje ka gaida Mum.”+ Ashraf ya dafashi yace ” next time kanina.” Murmushi sukai a tare Ashraf ya kira Dan Litti suka dau hanya, suna hawa kan titi dan litti ya kalli Ashraf yace ” Ashe ma kasan ‘yan gidan.” Ashraf yai murmushin takaici yace ” Gidan yayan mahaifiyata ne ” Dan litti yasa dariya yace ” ohh shiyasa yazo nan?” Murmushi kawai Ashraf yai ya bud’e window tare da kurama titi ido, suna isa gida ya fito jiki a sanyaye yai b’angarensa. Nafi kam harta gaji da jiran dawowarsa gashi ta mai abinci, ganin anyi sallar isha’i yasa tai tunanin dubawa ko ya dawo. Da yake yanzu tanada makulli bayan ta kwankwasa taji shiru sai ta bud’e kofar, duk wutan bangaren a kashe yake da alama ba mutum a ciki, ta d’an d’aga gira tare da yin ajiyar zuciya tace ” bai dawo ba.” Tayi nufin juyawa sai taji ringing din waya, ita kuma ba tata bace dan tata na gida, cikin tsoro ta fara…