ZUCIYA CHAPTER 18

ZUCIYA CHAPTER 18
ZUCIYA CHAPTER 18 Tun daga idanunsa take bi da kallo fuskarta sai murmushi ke bayyana, lalai soyayya da dadi amma batajin in har da wani ne zataji dadin soyayyar nan.+ Ashraf kam bacci ne ya daukeshi, jin yanda Nafi ke shafa masa kai. Bud’e kofar falon yasa ta kallo gun da sauri tana san ganin wanene ya bud’e kai tsaye. Ganin Anisa yasa ta zaro ido sai dai bataji zata iya d’aga Ashraf daga jikinta saboda Anisa. Itakam Anisa tun daga bakin kofa ta tsaya tana musu wani kallo, wani irin zazzafan kishi ne yake damunta, kitchen ta wuce direct ta debo ruwa cikin bokoti ta nufo Nafi. Itakam Nafi ganin tayi kitchen yasa ta saki numfashi na farin ciki, tare da kallan Ashraf, batai auni ba kawai sai ruwa sukaji akansu. A firgice Ashraf ya farka tare da mikewa tsaye, kallan mamaki ya shiga yima Anisa wacce ta shiga yin huccin masifa. Ya maida kallansa kan Nafi wacce dama kanta ba d’ankwali saboda dazu ya cire mata tun daga saman kanta har jikinta duk a jike yake jarab. Yaso yama…