ZUCIYA CHAPTER 17
ZUCIYA CHAPTER 17 Ashraf ya fita daga gun taron rai a b’ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace ” muje inkaika b’angaren baki ka huta ina da gun zuwa.”+ Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu. Ta ina zai soma nemanta??? Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, ina Nafinsansa? Little ce ta kirashi a waya wanda ita kanta ta kasa zama daidai saboda rashin Nafi, bayan Ashraf ya d’auka yace “ta dawo ne?” yai maganar cikin zumud’i. A hankali tace “a’a yaya.” Yai tsaki sannan yace ” to meye?” Cikin sanyin jiki tace ” yaya ina tunanin gidan kawarta ta tafi.” Da sauri yace “kawa?dama tanada wata kawa ne?” Little tace “Ferry wannan kawartata ta makaranta, ai a nan kano suke.” Ferry??? Tai saurin cewa kanwar Ya Nabil. Duk da yaji haushin inda akace take dan shi ya dauka saurayinta ne, amma yanzu gan…