ZUCIYA CHAPTER 16
ZUCIYA CHAPTER 16 Asim yana shiga bangaren Mahaifinsa yaga Mumy a zaune suna duba takardu, haushi da kishi ya kamashi ya karasa ciki a zuciye. Kawu ya kalleshi yace ” Asim meye hakan zaka shigo ko sallama?” Asim ya harari inda Mumy take ya kalli mahaifinsa yace ” in kuna tsoron Ashraf ni bana tsoronsa, sannan in ku bazaku iya komai ba akan halayensa ni zan gyara su.”+ Kawu ya daka mai tsawa yace “Kai wani irin hauka kakeyi hakan? Zakazo ka dinga fadamin zancen banza ko ni din abokin ka ne?” Asim ya kafe Mumy da ido yace ” gashi can dan da kuke ji dashi ya ajiye matarsa a titi ya zari karuwarsa sunyi gaba.” Hankalin Mumy ne ya tashi ta kalleshi tace “Bangane karuwa ba?” Asim yai wata dariya yace ” Au ke kika mahaifiyarsa bama kisa abinda d’anki yakeyi ba? Karuwarsa daya dauko daga wani kauyen nake nufi.” Mikewa Mumy tai tace “Nafi?bangane abinda kake nu……” Bata karasa ba taji ana zage zage a waje, Asim ya juya yai waje, kawu yai wani murmushi ta gefe sannan ya mike yazo kus…