ZUCIYA CHAPTER 15

ZUCIYA CHAPTER 15
ZUCIYA CHAPTER 15 Ganin yanda jikin Nafi yai sanyi yasa Little tace ” Me ya ce miki?” Nafi tai murmushi tace ” tambaya ta yai kawai yaushe zamu dawo nace wasu yau mukuma sai gobe.”+ Little ta dan tab’e baki tace ” akan haka ne naga ya zuciya?ni wlh na d’aukama ko laifi kikai.” Habib yai dariya yace ” kinsan yayan naki ai Gimbiya.” Haka dai sukai ta hira sama sama sannan sukai sallama tare da tafiya da kayan Nafi yanda gobe sai dai ta taho ita kad’ai. ******** Shikam Ashraf har ya isa gida zuciyarsa batai sanyi ba, sai ma kara tunano abinda tamai kawai dayakeyi, sannu yaya? Lalai kalman nan ta bala’in b’atamai rai ya cije leb’e tare da yin kwafa lalai yarinyar shi zata dizga??? Da karfi ya shiga gidan ko mai gadin bai kalla ba ya fito tare da rufe kofar motar da karfi yai bangarensa. A falo yaga Anisa tana ganinsa ta taso da sauri tana neman rungumeshi gocewa yai ya wuceta yai gaba. Kallan takaici ta bishi dashi tana kallo ya shige d’aki tare da rufo kofar da karfi, wan…