ZUCIYA CHAPTER 12
ZUCIYA CHAPTER 12 Yanda yake kallanta yasa ta had’e rai tare da maida kallanta wajen window, itakam batasan me zata cemai ba, ana san kashe ka? Kuma ‘yan uwanka?? Itakam kalaman nan sun mata tsauri.+ Ga mamakinta jitai yace ” tunda karyar ciwo kikai yanzu ai sai ki koma gida.” Nafi ta kalleshi a tsorace tace ” Sauka zanyi a haka??” Kai ya d’aga mata alamar yes, idanunta ne sukai rau rau ta kalleshi sannan tace ” taya zan iya fita ahaka komayafi fa babu a jikina, sannan bani da kud’in da zan tafi da kaina.” Ya d’aga mata kafad’a alamar wannan kuma ruwanta ne, Nafi ranta ya b’aci a zuciye ta matsa da niyyar bud’e kofa, har ta zura kafa d’aya zata fita sai taji yace ” shigo in ajiyeki ba dan halinki ba inada abinyi.” Ta koma ta zauna kamar ba taso sai dai ko kallan inda yake batai ba, Ashraf ya tada mota zuciyarsa fal da tunani, har suka isa gida ba wanda ya sake magana, yana parking ta bud’e kofa zata fita sai kuma ta juyo tace ” Yaya ina zaka?” Kallanta yai yace ” banaji w…