ZEHRA CHAPTER 9
ZEHRA CHAPTER 9 MUHAMMAD OMAR TAFIDA RESIDENCE Wata daya kenan da aka daura auren nasu. Tsawon wata daya Zehra tana kwance tana fama da radadin zuciya.+ Gaba daya ta bi ta zabge. Tayi qoqarin yin haquri amma kuma ta kasa. A kodayaushe zaka ganta riqe da wayar ta tana kallon hotunan shi. Idan bacci take yi zaka ji tana ta surutai wanda kuwa idan ka saurara da kyau duk maganar Mustapha take yi. Anty ta so a hada ta da therapist amma Papa ya hana. A cewar shi she will get over the shock. Ganin ta qi responding to present situation ne ya yanke hukuncin kai ta gidan mijin ta. Its better she faces reality maybe she will get over her depression faster. A yau ne da yamma aka kawo ta gidan wanda kuwa Papa da kanshi ya kawo ta. Fadeela, Hidaya da Khadeeja sune suka zauna da ita har zuwa dare wanda zasu tafi. Tunda aka kawo ta kuwa take kwance cikin duvet tana ta kuka. A yau dai ta tabbatar lallai Mustapha ba nata bane tunda har aka kawo ta wani gida a matsayin matar aure. Ta tabbatar Mu…