ZEHRA CHAPTER 7
ZEHRA CHAPTER 7 EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE Kwance take a kan kujerar tana ta kuka yayinda Hidaya take ta bata haquri.+ Sossai Hidaya take mamakin irin soyayyar dake tsakanin qawarta da Mustapha. A rayuwarta bata taba ganin dedication a soyayya irin nasu ba. Ji nayi Hidaya tace “Babes wannan tafiyar da zai yi ba wai yana nufin ya rabu da ke bane fa, you know cewar he is yours, why are you this bothered??” Cikin kuka Zehra tace “Babes wallahi ni kaina na rasa dalilin da ya sa na kasa samun natsuwa, kawai ina feeling kamar I am about to lose him” Hidaya wadda ta tausaya ma halin da take ciki tace “please calm down my friend, the guy is yours and yours alone, Insha Allah zai dawo zuwa gare ki in no time” Da haka dai ta cigaba da lallashinta tare da fadi mata kalamai masu sanyaya zuciya har ta haqura. ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Ko da Mustapha ya iso gida a gurguje ya qarasa sashen shi yayi wanka sannan ya shirya cikin wata tsadaddar shadda sky blue mai kyan gaske…