ZEHRA CHAPTER 6
ZEHRA CHAPTER 6 EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICES Mustapha ne yayi parking motar shi a Parking lot.+ Tun Kafin ya qarasa fitowa ne Ma’aikatan wurin suke ta kawo mishi gaisuwa cike da girmamawa yayinda yake ta amsawa amma fa fuskar shi a daure domin kuwa shi kam asalin shi ba mai yawan fara’a bane. Idan ka gan shi yana murmushi harda dariya toh fa Lallai Zehra ce take kusa da shi. Wurin yana functioning sossai musamman bangaren small Chops. A yau ma kamar kullum mutane birjik ana ta siyan abubuwa yayinda wasu suke tafiya da shi wasu kuma suna zama a nan su ci. Mustapha a ranshi yace “Kowa da abinda yake so, ita kuma My Angel ta rasa abinda take so sai irin wannan” Girgiza kai yayi ya haura sama. Ko da ya qarasa lounge din office din ya samu Salima Secretary dinta zaune akan table dinta yayinda take ta aiki a computer. Tana dago kai kuwa ta gan shi ne tayi saurin miqewa tace “Ina wuni Sir” tare da russunawa. Yace “lafiya, is your madam in?” Tace “yes sir, suna Meeting ne am…