ZEHRA CHAPTER 5

ZEHRA CHAPTER 5
ZEHRA CHAPTER 5 ABU-YAZEED RESIDENCE Zaune yake a kan stool din Vanity table na dakin yayinda ya cika da tsananin damuwa. Kusan awa daya kenan yana nan zaune yana ta kallonta yayinda take ta motsi cikin bargo tana bacci.+ A yau ne Mustapha zai yi tafiya zuwa Lagos har tsawon sati daya. Kamar yadda yayi mata alqawarin zai zo suyi sallama kuwa ya zo amma kuma ya tarar da labarin cewar bata da lafiya tun cikin daren jiya. Babu yadda Mustapha bai yi da Anty a kai ta asibti ba amma kuma sanin abinda yake damunta ne yasa Anty tace kar ya damu zata samu sauqi. Tun kafin Fadeela ta tafi wurin aiki Mustapha ya zo gidan. Har tana yi mishi tsiya wanda he didn’t find funny, mamaki ma ya dinga yi na yadda basu dauki ciwon nata serious ba. Anty ce ta shigo dakin ta same shi zaune ya sa mata ido. Gani nayi tayi dariya tare da matsawa kusa da shi tace “hey, gwara ka tashi ka kama hanya, kar kayi missing flight dinka. Ka dai san na fadi maka she will be fine ko? Trust me she will” Ba tare…