ZEHRA CHAPTER 4
ZEHRA CHAPTER 4 ABU-YAZEED RESIDENCE A yau kwana daya kenan da aka sallami Zehra daga asibiti. Tunda ta dawo kuwa take ta hutawa domin kuwa Zain ya bata hutun bed rest na kwana uku kafin ta cigaba da al’amuran ta. Wuraren qarfe goma sha daya na safe tana kwance a cikin bargo tana replying messages din mutane wanda suke ta wishing dinta quick recovery yayinda take hira da qawarta Hidaya wadda ta zo gaishe ta. Fadeela kuwa ta je aiki yayinda Khadeeja ta tafi school. Baraka mai aikin su ce ta shigo riqe da wani cute bouquet na white flowers da wata ‘yar qaramar takarda a ciki. Zehra wadda ta sa ma bouquet din idanuwa ce ta tashi zaune da sauri tace “wow, Baraka daga ina haka??” Baraka ta qarasa wurin ta tace “Anty dama Hajiya ce ta bani in kawo miki” Da sauri ta miqa hannu tace “bani in gani” Baraka ta miqa mata yayinda Hidaya tace “I have never seen a bouquet this cute, babes waye ya aiko miki? dama kina da boyfriend kike ta boyewa ko?? Allah ya kama ki” 4 Zehra wadda…