ZEHRA CHAPTER 15 KARSHE
ZEHRA CHAPTER 15 KARSHE MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE Wuraren qarfe goma da rabi na safe kwance take a kan gadon yayinda yake maqale da ita. Kanshi a bisa qirjinta yana ta bacci yayinda take rungume da shi kamar wadda take tsoron kar a sace mata shi.. Kusan mintuna talatin kenan da Zehra ta farka amma a dalilin bata so tayi interrupting baccin nashi ne ta qyale shi. Bata ankara ba ta ji ya dan motsa, da alama ya farka ne. Jin yayi shiru ne tace “Baby??” Yace “na’am” Tace “ka tashi ne?” Kai tsaye yace “a’a” Fashewa tayi da dariya tace “baka tashi ba?? Toh da wa nake Magana??” Muryar shi qasa-qasa yace “My Angel bana so in tashi ne, duk tsawon rayuwa ta ban taba yin bacci mai dadin wannan ba, I feel kamar in cigaba da bacci a jikin ki har abada” Zehra wadda ta qara matse shi a jikinta tace “Baby my body is all yours, so duk yadda kake so kayi da shi zaka yi… anytime! amma yanzu kayi haquri muyi wanka sai mu yi breakfast.. Ka ji??” Kai tsaye yace “bana jin yunwa” Tace “wallah…