ZEHRA CHAPTER 14

ZEHRA CHAPTER 14
ZEHRA CHAPTER 14 EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE Tsaye take a wurin window din office dinta yayinda take hangen shi zaune yana ta jiranta.+ A yanzu Mustapha ya hana ko wanne driver fita da Zehra sannan ya hana a dauko ta. Ya basu strict warning akan idan har ta kira su toh su sanar da shi. He has taken the responsibility na kai ta duk inda zata je as long as he is around. A yanzu kuwa yana cikin hutu ne wanda aka bashi har na tsawon wata biyu don huta gajiyar course din da yayi na tsawo shekara hudu don haka he is always available. Kusan minti talatin kenan yana zaune a waje yana jiran ta. 7 Mustapha dai ya sani sarai Zehra ta san ya zo domin kuwa har ma’aikatan ta sun sanar da ita isowar shi amma saboda bata so ta bi shi shiyasa ta qi fitowa. Sossai ran shi ya baci da hakan amma dayake Zehra ce he was trying as much as possible to control himself. Hidaya wadda ta shigo office din ne ta gan ta tsaye jikin window yayinda tayi nisa a kallon shi. Ko da ta zagayo don ganin …