ZEHRA CHAPTER 11

ZEHRA CHAPTER 11
ZEHRA CHAPTER 11 It’s never nice to lose someone close to you; unfortunately, life goes on, and we have to make peace with it and move on” + ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Allahu Akbar!!! A wannan safiyar hankula sun tashi, Zuciyoyi sunyi sanyi yayinda suke ta juyayin rashin Muhammad. Tabbas duniya wuri ne na wucewa ba na wanzuwa ba, gidan wucewa ne zuwa gidan tabbatuwa sannan babu wani wanda ya isa ya qi tafiya. Babu shakka mutuwa riga ce wadda ba ta fita, ta ma fi qarfin a kira ta da riga domin kuwa fatar jiki ce da ba a iya yage ta a jefar. Kowane mutum yana da qarshe mai zaqi ko mai daci. Mutuwa ta tafi da Muhammad ta bar mu da juyayi. Gaba dayan su tun suna kuka da hawaye har hawayen ya qafe. Wuraren qarfe bakwai na safe aka shirya Muhammad aka yi mishi sallah. Mustapha kuwa har a wannan lokacin bai yi kuka ba, da alama he is still in shock. An kira Mummy, Anty da Fadeela sun je sunyi mishi addu’a wanda kuwa sai riqe su aka yi aka fitar da su domin kuwa Fadeela ma suma tayi yayinda qa…