TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 9
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 9 Cikin iko na Ubangiji da taimakon wata malamarsu Dr. Mu’azatu Usman El-Yakub ta samu tayi differing semester ɗin nata, hakan ya sanya ta daina fita makaranta.3 Cikinta kullum girma ya ke ƙarawa yayin da motsinsa ta zama mata abokin hira abokin ɗebe kewa. Idan ya motsa har shafo shi take cike da ƙauna ta ce “Ubangiji Allah ya nisanta ka da mummunar halin mahaifin ka” wani lokaci kuma ta shagala wajen ba shi labarin duniya.4 “ka ga rayuwar duniya da daɗi amma cike yake da ƙalubale, kar ka damu ina son ka, ba zan taɓa juya maka baya ba, come sun come rain” ire-iren hirarrakin da ta ke yi da ɗan Cikinta kenan. Wani lokaci ta bashi jinsin mace wani lokaci na namiji.4 Banda pad, zaitun, sai riga ƙwaya ɗaya bata ta siya komi ba, su ɗin ma da kyar ta iya fitar da kudin su saboda gaba ɗaya ba ta da hanyar samu.5 Saifullahi kuwa sashin da aka tura shi aiki babu wani tsauri, ya kan yi sati biyu bai je Abuja ba in ya je kuma baya wuce kwana biyu zuwa u…