TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 8
TAZARAR DAJE TSAKANINMU CHAPTER 8 Ko da ta fito tashi yayi tsaye su ka fice, a mota ya kira Salis ko yana asibitinsa kasancewarsa likita ma’aikaci a asibitin gwamnati na Gambo sawaba, mahaifin sa kuma ya buɗe masa nashi a cikin GRA, mutane na son asibitin saboda kwarewarsu da kula da marasa lafiya.+ Minti Ashirin ya ɗauke su kafin su ka isa Umjad clinic and maternity. A dirare Amatullah ta gaida Salis don cike take da waswasi duk da cewa a shirye take da ta yi komi don farin cikin mijinta. Ai ko ba komi Aljannarta na ƙarkashin ƙafafunsa ne, da wannan take ba kanta haƙuri da ƙwarin gwuiwa.5 “Bari mu yi scan mu ga girman cikin don kamar ya fi wata ɗaya fa” Salis ya ce bayan ya ɗan dudduba ta. “Kai likita ban son shegantaka, watan nan ne kawai ta yi ɓatan sa amma duk saura suna zuwa” Saifullah ya ce a ƙufule, shi kawai so yayi a mata allura ko ya bata kwaya ta haɗiya cikin ya zube.3 “Engr. Ai wasu ma har su haihu su na yi, wasu in sun kammala wata ukun farko, wasu sai ya kai s…