TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 7
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 7 Rana ɗaya aka yi komai aka gama. La’asar na yi Baban Sasa ya ce a shirya amarya a kai ta ɗakin mijin ta. Nan fa amarya kuka har da majina, musammam da aka ce ta zo ta yiwa Gwaggo sallama.2 Hannayen ta biyu ta sa ta riƙe ƙafar Gwaggo da kyar aka iya bambare hannun aka wuce da ita ɓangaran Hajiya. Nan kuwa ruwan habaice habaice su ka sha daga dangin Hajiya. Haka ma Hajiya wacce ta dubi Amatullah da ke tsugunne gaban ta fuskar ta rufe da lafaya, buɗar bakin ta sai cewa ta yi ” Toh mu dai babu abin cewa tunda ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, Allah dai ya sa za ki iya kula da mijin na ki, dadin ta dai namiji mijin mace hudu ne…..”2 “Bare ma ɗiyar ta mu ai san kowa kin wanda ya rasa ce, wajan kula da iya zaman duniya ba a ce mata komai, uwar gida sarautar mata ba, kowa ya zo bayan ki ya ke….” Cewar kanwar Gwaggo yayinda yan uwa Gwaggo su ka kara karfafa mata gwiwa da guɗa. “Toh ai sai ku tashi a kai ta, Allah ya sa a dace” “Allahumma amen…