TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 6

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 6
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 6 Tun tana tsumayen Zulaikha har ta tabbatar da ba za ta dawo a ranar ba, hakan ya sanya ta zama sukuku kamar raguwar ciwo, duk yanda ta so kar ta zurfafa tunani ta gaza hakan ya sa ta ɗauki littafin da ta fi so watau Don’t be Sad ta fara bibiyar hikimomi na samun nagartaccen kwanciyar hankali,da haka bacci ɓarawo ya sace ta.2 Washegari Monday basu da aji sai ƙarfe tara na safe, hakan ya sanya ta ɗaukan lokacin ta wajen shiryawa. Takwas da rabi daidai ta fita daga hostel. Sauri take don ba ta fatan ganin Dee. Ta kai daidai biological science da za ta bi ta je chemistry department in da za su yi ajin ta jiyo sallama. Ƙara sauri ta yi don ba ta da niyyar tsayawa duk da sautin muryar kamar wanda ta sani. “Anty Amatullah an tashi lafiya” ya faɗi hakan ya sanya mata juyawa, tana ganin fuskarsa ta juya cikin sauri ta cigaba da tafiya. Ba za ta ce ga yadda aka yi yazo gabanta ba.2 “Don Allah kiyi hakuri, wallahi na yi tunanin ya faɗa miki ne shi y…