TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 4

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 4
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 4 Kamar saukar aradu haka maganar Dee ya sauka kunnen Hajiya, wacce ta yi ƙaryan zagawa bayi amma ta ɓige da zuwa soro domin ganin wannan saurayi da Baba Anas ke ta zuzutawa, wato wanda aka zaɓa akan Saifullah. “Sanadiyyar abin da ya sami mahaifiya ta, Ni da ke Amatullah kowannan mu za mu iya yin addinin mu, Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki, ki dubi girman Allah ki amince da aurena… ” Kalaman da ke mata yawo cikin kwakwalwar ta kenan, musammam jin Dee ya ce “Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki”4 “kenan shi ɗin ba musulmi bane” ta faɗi tana mai toshe bakinta kamar ba ta son wani ya jiyota. Matsar da kunnenta tayi tana so ta jiyo wani abin da zai tabbatar da zarginta. Babu abin da ta jiyo sai shesshekar kukan Amatullah, ta tsaya kusan mintuna uku tana jiran jin abin da za ta ce amma shiru sai kukan da take yi. Hakan ya sa ta juya don ta koma cikin gida jikin ta na rawa tsabagen daukan gulma.5 Amatullah kuwa kuka ne ya ci ka…