TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 3
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 3 Salamun alaikum”+ Ta faɗa cikin faɗuwar gaban abin da zai biyo baya. Juyowa yayi fuska murtuke, bin ta yayi da kallo tun daga sama har kasa, irin wannan kallon na hadarin kaji.4 A wulakance ya amsa da “Waalaikumus salam, na baki minti goma cal ki haɗo kayanki ki fito” Iya abinda ya ce kenan ya buɗe mota ya shige. “Ki haɗo kayan ki mu tafi?” Ta daɗa nanatawa cikin ranta, shikenan ta faru ta ƙare ramamme ya zagi maye. Karfin hali ta yi ta ƙarasa jikin motar, da ya ke ya ɗaga gilashin sai ta kwankwasa a hankali. Sai da yayi minti biyar kafin ya sauke tare da faɗin “Menene kuma? Ba ki ji abin da na ce ba ne?” “Dama cewa na yi ya jikin Baban Sasa?” “Oh so ki ke na ce ya mutu ko? Toh ya nan daram da ran sa……”6 “Alhamdulillah” Amatullah ta furta ta na mai ajiyar zuciya ta juya ba tare da ta sake tambayar ba’asi ba. Tana zancen zuci ta isa hostel, har ta wuce shi ba ta sani ba sai ji ta yi ya kira sunan ta “Amatullah?” J…