TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 13 KARSHE

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 13 KARSHE
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 13 KARSHE In da Dee da Amatullah su ka yi kwanan farin ciki, Saifullahi da Ayush a nasu ɓangaran kwanan tashin hankali su ka yi, Dan kuwa Saifullahi ranar kamar wanda aka yiwa mutuwa, wani bakin kishin yau Amatullah za ta kwana da wani ba shi ba ne ya addabi rayuwar sa. Matar shi da ta gane yanayin da ya ke ciki ba ta saurara masa ba, ba ta yi la’akari da jama’ar biki da ke gidan ba haka ta ringa neman sa da tashin hankali ta na mai daga murya. Sai barin ɓangaren sa yayi, ya koma falon Baban Sasa, nan ya sha kukan sa ya koshi kamar yaro dan goye. Yanda ya ga dare haka ya ga rana.2 **** Sai da Amatullah ta yi kwana uku a gidan ta, a daren na hudu su ka raya sunnar manzon Allah SAW, cikin aminci da yardan juna, so da kauna tare da tausayi. Farin cikin da Amatullah ta ji ko rabin sa ba ta ji ba sanda ta kasance da Saifullahi a daren su na farko. Dee ya mata alkhairi babu adadi, ya Kuma mata albishirin zuwan su umarah da za su yi wata mai zuwa. T…