TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 11
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 11 Gaba ɗayansu bin sa su ka yi da kallo har ya fice, nan ne Baba zubairu ya ɗan muskuta ya ce+ “Nifa ban ga laifin yaron nan ba, na tabbata da ace shi mu ka gani a wannan hali ba zamu taɓa waiwayensa ba balle mu taimaka masa, bayan mu ne addininmu ya koyar da mu kyautatawa” yace yana mai kallon ƙanensa zuciyarsa cike da Nadama. “Gaskiya ne, don wallahi ba ruwan bambancin addini a kyautata mu’amala ko sauke hakkin makotaka. Yanda ya wajaba a kan musulmi haka ya wajaba akan wanda ba musulmi ba, sannan a ko ina cin fuska haramun ne” Baba Anas ya ce yana mai goyon bayan Baba Zubairu. “Amma kuma aka ce kada mu riƙe su aminai” Baba hamza ya ce a ɗan hasale.. “Eh an ce kada ka rike su aminai don za su cutar da kai amma ba a ce kada ka rike su da amana ba, kun manta zamanin Annabi SAW sau da yawa kafirai na zuwa da niyyar kashe shugaban halitta amma su ɓige da musulunta ba su kaɗai ba har mutan garin su, duk saboda kyakkyawan mu’amala da musulunci ya ko…