TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 10

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 10
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 10 Hawaye bai daina zuba daga idanun Baban Sasa ba yayin da ya ke duban Saifullahi, cikin dashassheyiyar murya ya furta+ “Saifullahi har ka iya buɗar baki ka furta saki ga Amatullah? Ashe za ka iya sakin Amatullah?” “Kukan nan na ka shi ke ɗaga mana hankali Baba, dan Allah ka sawa zuciyar ka salama ɗan yau ba a biye masa, sai ya kara ma ka ciwo” Cewar Baba Zubairu cikin rarrashi.4 “Ni kuwa na ke iya masa! Kai waye nan! Hafiz! Hafiz! ya ka nan!” Baba Anas ne ya shiga kwallawa Hafiz Kira, in da ya shigo da saurin sa dama nan soro yayi laɓe ya na jin komai.2 “Je ka kira min uwar yaron nan!” Ya fada ya na mai nuna Saifullahi da ɗan yatsa. Gaban Saifullahi ne yayi mummunar faɗuwa ganin Hafiz ya fita da sauri, cikin sanyin murya ya ce4 “Dan Allah Baba….” “Dakata! Ba na so na sake jin ka tanka a nan idan har ba ni na ba ka izini ba!” Jin haka Saifullahi ya sunkyar da kai. Amatullah kuwa burin ta a sallame ta shiga gida ta mike kafa ko ta sami sauk…