SAMU YAFI IYAWA CHAPTER 7 KARSHE
SAMU YAFI IYAWA CHAPTER 7 KARSHE A cikin daren abubuwa suka dame sam ya kasa runtsawa juyi kawai yake yi yana tuno abunda nace masa na bazan bishi kano ba,.. Ko da ya zo da safe ma Haka na turje,dama gashi idan ya zo gidan ma sai na ja masa rai sosai kafin na fito na same shi kuma magana daya nake yi bazan bishi kano ba, Har yanzu babu sauki. Shi dai har yau yaki gya makowa me muke ciki a tunanim sa zai iya shawo kaina da kalamai cikin sauki”Jiya da shike yasan ana saura kwana daya satin da suka deba min ya kare sai ya zo min da salon magana cewa zai sauya min gida na zauna ni kadai in ma zama da zuwairah ne bana so ,nikuwa a ranan na fito fili na gaya masa yanzu “ni bana son sa ne kawai zan kuma so ya sake ni na huta bazan iya daukar komai ba…”2 Ni kaina na sha mamakin taurin zuciyar da nayi masa ina magananga nu wanda mafi akasari nasan bakara min ciwo suke masa ba., don yasan ya aikata min abunda ya kamata na guje sake zama da shi din.. Shima yaki sam ya amince da hakan,…