RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 6 KARSHE
RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 6 KARSHE Driving sawwam yake da hannu daya yayinda daya hannun kuma yake rike da hannun abar kaunarsa ummulkhairi, “My lonely nasan jiya bakiyi bacci ba kamar nima yanda banyi ba ko?” Yace da ita yana murza yan yatsunta, Idanuwanta ta lumshe ta sake kwantar da kanta ajikin kujerar da take zaune, “Wallahi banyi bacci ba sawwam, ai nariga da nayi sabon da bazan iya bacciba sai tare dakai..” Murmushi yayi ya dan kalleta kafin ya mayar da idanuwansa kan titi, “To kuma my lonely ranar da kuka zama ku biyu yaya zakiyi?” Yace da ita cikin zolaya harda fakar idonta yayi mata gwalo kasancewar idonta arufe yake shiyasa bata ganshi ba, “Mu biyu kuma? Ai ko yanzu ma mu biyune” tafada idonta har lokacin arufe yake, “Ah wai ina nufin idan na kawo miki kanwa” Murmushi tayi tafara zare hannunta daga cikin nashi, “Nabar mata kai tun kafin tazo” Dariya yayi ya juya ya kalleta, “Tun da wuri haka har kin bada ni kyauta” Shiru tayi masa fuskarta kunshe da murmush…