DA'IMAN COMPLETE

DA'IMAN COMPLETE
DA’IMAN COMPLETE Sallama take kwadowa tun akofar gidan harta shigo dan karamin tsakar gidan. Sanye takeda atampha ‘yar leda kalar kore shar wato kalar asalin ‘dan ‘kauye..sai wani gyale fari data yafo mai bakin lesi da ‘yar jakar hannunta ‘baka data farfashe alamar tsufa duk da itace tafi kowa wayewa akauyen tunda itake zuwa birni. Shekarunta xasu kai talatin da takwas zuwa da arba’in zuwa da sama. Wata sallamar takuma kwadawa tana fadin, Wai duka gidan bakowane nake sallama ba’a amsawa? Daga bayanta taji an amsa mata cikin wata yar siririyar murya. Juyowa tayi adan tsorace tana ganinta ta hade fuska tareda watsa mata harara tace, Lallai na yarda da kinsamu sake a wurin ladingo. Munafuka mai kamada mayyar uwarta ace kina cikin gidan nan naketa rangada sallama amma kikayi lukus a daki. Toma wai uwar me kike adakin ne. Sunkuyar da kanta tayi muryarta na ‘dan rawa tace, Kiyi hkr iya jummai wlh kainane yake ciwo banjiba. To dama ina zakiji ladingo ta daure miki gindin iya shege. Lad…