YANAYIN RAYUWA CHAPTER 12
?YANAYIN RAYUWA?????????. CHAPTER 12 By halimatusadiya Saleh? ” Wowww!” Abunda maryam tace dataga wayan,aunty hapsat tace ” A gaskiya yayan namu naji dake fa.” Wani irin murmushin dole zali tayi,ta fada kan gadon ta kwanta. Maryam tace ” Kwanciya kikayi,maza tashi muje mununa ma mom.” Tafada tana faman kama hannun zali,fisge hannun ta tayi tace ” Ni kibarni barci nakeji.” Tsaki maryam taja,ta karbi wayan a hannun aunty hapsat ta wuce dakin mom. Tasamu mom na shirin kwanciya,jin salama yasa tajuya ,taga Maryam rike da waya. Karasowa maryam tayi tace ” Mom kalli wayan da ya Umar yasama zali.” Karba tayi da murna tace ” Masha Allah,yayi kukari.” Murmushi Maryam tayi tace ” Mom gaskiya wayan yanada kyau sosai.” Mom tace ” Allah yayi Albarka. ” ” Ameen” Maryam tace kafun tayi ma mom sallama ta fita. Kaman yanda ta barsu haka ta samesu sede. Bama zali wayan tayi tace ” Natayaki murna asufar lafiya.” …