UZTAZIYA KO YAR DUNIYA COMPLETE
UZTAZIYACE KO YAR DUNIYA . COMPLETE Damko gashin kanta yayi yayinda ya Kara gwara shida bangon bayin a karo na biyu cikin wahalalliyar murya take ihu hawaye masu zafi nabin fuskarta, kazamar banza yar’iska ragowan Gayu Dan ubanki maina gaya miki kafun inbar gidan nan? Juyo da fuskarta yayi yayinda ya daga habarta matse bakinta yayi cikin masifa ya hankado ta wajen bayin saida ta buga kanta da kujerar dressing mirror take kan nata ya shiga zubda jini, kasa jurewa tayi jin azaban take har cikin kwakwalwarta hakan yasa ta Saki ihu tareda tsugunnawa tana murza hannayanta biyu Alamar hakuri, ‘Dan girman Allah AK kayi hakuri na tuba nabi Allah nakuma bika mijina ka yafe mun, takowa yayi har inda take yayinda take matsawa baya saboda gudun azabar dazai Kara manna mata, damko gashin kanta yakara yi tareda janta a kasa har bakin gadon dake dakin ya zauna yana ware kafafuwan shi duka biyu, fuskarta datayi jaga jaga da jini da majina yakara dagowa hadeda kai fuskar shi saitin bakinta ciki…